Ma'anar Trade Na Cyptocurrency






Cyptocurrency: wani kudi ne da ake amfani da shi wajen hadahadar kasuwanci, wanda shi wannan kudin baya karkashi gwamnati, duba da kudin banki yana karkashin kuwalar gwamnatin kasa ne amma shi. Crypto Currency. Baya karkashin ikon. Gwamnatin kowace kasa.

Anyi amfani da kalmomi biya ma'ana. Crypto da kuma Currency. Sabida da mai yasa akayi amfani da Cryptocurrency a matsayin sunan wannan kudi?

Shi dai cypto a ma'anar da tafi dacewa da shi a wannan fannin shine (Ɓoyayye) shi kuma Currency: kudin da aka yarda ayi amfani da su, idan muka fassara cyptocurrency gaba daya zai iya bamu (Ɓoyayyan Kudi)

Ma'anar ɓoyayyan kudi shine: kudin da ba'a iya ganin su a zahiri amma za iya ganin su a rubuce ma'ana za iya ganin Numbers na wannan kudi, su kuma kudin da ake ganin su a zahiri sune kudin da zaka iya taɓa su kamar kudin takarda da kuma kudin fata ko na leda. 


Shi Cryptocurrency. Kudi ne wanda aka ƙirƙiro shi sabida cinikayyar online amma maganar gaskiya wadanda suka fi amni da shi wajen kasuwanci sune kamfanunuwa, duba da shi bashi da wani iyaka wajen yin ma'amalar turawa da turowa, ma'ana zaka iya turawa abokin kasuwanci ko nawa kake da bukatar tura mai ba tare da gwamnatin kasar ka ta san da wannan kasuwancin ba, hakan yasa masu amfani da manyan harƙallolin da suke da amfani harma da wadanda haramtattu ne suka amfani da wannan kudi na. Crypto Currency.


Sannan akwai wadanda suke samun kudi da shi ta hanyar yin trading sabida shi kudine mai ƙaruwa da kuma raguwa a koda yaushe hakan yasa wasu keyin trading idan sun siya sukaga kudin su ya karu sai su siyar da shi wannan abunda suka siya (Coin), ga masu bukatar sanin mai ake nufi da trading zasu iya ziyartar shafin Trade a wannan manhajar


Cyptocurrency da bank

Alaƙar Cyptocurrency da bank account, wasu da yawa suna cewa taya zasuyi ma'ala da kudin Crypto Currency da kuma kudin bank account nasu, 

Shidai wannan kudi na. Cyptocurrency wasu ƙasashen sun yarda da shi wasu kuma kasashen basu yarda da shiba kuma duk ƙasar da bata yarda da wannan kudi na cyptocurrency ba to tana kowa dalilin ta na ƙin yarda da shi wannan kuɗin.


Duba fa haka ne wasu kasuwan nin Crypto Currency ɗin sukeyin P2P.

Ta hanyar P2P mutanan kasar da bata amince da kuɗin cyptocurrency ba suke amfani da shi, P2P wata hanyace wacce zakayi ma'aka da Crypto Currency ba tare da sanin kasarka mai kayi da wannan kudin naka ba na bank account  sabida shi P2P kamar kasiyi abune kayi wa mutumin da kasiya abu a hannun sa Transfer din kudin amma idan kayi deposit da card naka to tabbas wannan abun sai ƙasarka ta san me kayiwa deposit hakan yasa ƙasar da bata yarda da wannan kudi ba na  Crypto Currency. card na ƙasar nasu baya iya deposit a harkar. Crypto Currency. Sai dai P2P.


Bitcoin

Shi dai Bitcoin shine babban duk wani kudin da aka kirkire shi domin yin kasuwancin online dashi, sabida a yanzu idan kana da kamfani kuma kana son a sayi kayan ka da. Cryptocurrency. na kamfanin ka to fa shi wannan kudin daza ka kirkira dole sai ya zama a karkashin Bitcoin


Bitcoin wani bawa mai suna. Nakamoto shine ya ƙirƙire shi ya samar da code na bitcoin tun 2007 zuwa 18 August 2008 sannan abokin aikin sa yayiwa wannan bitcoin din rigistar website mai suna bitcoin.org, bayan fitowar bitcoin shi wanda ya kirkire ya boye kansa hakan ne yasa wasu daga cikin mutane sukai ta fitowa suna kiran kansu da. Nakamoto kuma karya sukeyi


Wannan bitcoin din yasamu karbuwa a duniya kuma a yanzu haka ana samun amfanuwa dashi domin ta silar sa da yawan mutane sunyi arziki, wasu malaman sun haramta siya da siyarwar sa wasu ku sun halakta shi. (Abu mafi inganci shidai wannan bitcoin din siya da siyarwa ne)


Bitcoin tun lokacin da aka ƙirƙire shi bai taba samun kishiya ba sai a wannan karan kishiyar da yasa samu shine Pi Network wanda a yanzun haka ana mining na wanna pi network din shima shima Bitcoin haka akayi mining nasa farkon fitowar sa wanda har yanzu ana yin mining dinsa ba'a dai na ba, kuma haryanzu ana ƙirkiro sabbin coins a karkashin s




Ma'anar Trading Na Coin

Shi coin a koda yaushe tafiya, da tashi, da suka, yake yi kamar wani jirgi amma tafiyar ta shi tasha bamban da ta jirgin sabida tafiyar ta shi ta hawa da sauka ne ma'ana tashin farashi da saukar farashi misali coin yana naira 1.00 sai ya koma naira 1.01 ko 1.03 ko ma sama da hakan,wajen sauka kuma zai iya komawa 0.93 daga 1.00 ya danganta da kalar irin coin din da aka siya da kuma farashin sa, to masu siyan sa daga 1.00 zuwa 1.03  ko 1.05 ko ma sama da hakan a lokaci ƙanƙani ko lokaci mai tsayon da bai wuce watanni ba, masuyin wannan su ake kira da masu yin trading idan kuma yakai shekaru sun koma holders


Taya ake samun riba a trading

Ana samun kudi ne a trading idan ana da jari masu yawan gaske sabida idan ba a da jari masu yawan gaske saidae a samu na garau garau amma ba makudan kudi ba bari in danyi muku misali. Idan ka siyi coin na 10M a lokacin da aka siya yana farashi naira 1.00 zai iya komawa 1.05 cikin minti 30 ko awa 1 to idan kayi lissafi zakaga 0.05 ya karu a cikin kudin ka to wannan 0.05 din ita zaka lissafa ta iya adadin kudin da ka zuba tofa iya adadin ribarka kenan. A cikin lissafin mu 0.05 sau 10M zai kama naira N500,000 kenan idan ace ana da jarin da yakai 10M to a kullum za'a iya samun kudin da ya haura 1M.


Sannan shi trading bashi da hadari ko a sarar kudi kamar forex saidai idan kaga kayi asara to fa baka da hakuri ne ko kuma ka bukaci kuɗin da ka zuba a lokacin da coin din da ka siya bai tashi ba

Ga wadanda suka san trading kullum suna yinshi ne a matsayin sa'ar su sannan kuma shi coin kullum cikin tafiya yake kuma tafiyar tasa karantar ta ake idan dai har ka karance ta to fa zaka samu kudi idan kana da jari. Zamu lissafo Kadan daga cikin tafiyar kowane irin coin wanda yake ƙarƙashin bitcoin, akwai kamar su

*Reversal Patterns*

1 - Double Top

2 - Doube Bottom

3 - Head and Shoulders

4 - Inverse Head and Shoulders

5 - Rising Wedge

6 - Falling Wedge


*Continuation Patterns*

1 - Rising Wedge

2 - Falling Wedge

3 - Bulish Rectangle

4 - Bearish Rectangle


*Bilateral Patterns*

1 - Ascending Triangle

2 - descending Triangle

3 - symmetrical Triangle

A cikin wadannan da muka lissafo ko wanne karantar su ake sosan gaske bayan wannan akwai wani karatun wanda ake kiran sa. Candlestick Pattern. wanda shima yana da yawan gaske amma shi wannan wadanda suka fiya amfani da shi sune masu yin Trading na dan ƙaramin lokaci da kuma masu Forex Trading


Forex Trading

Shi forex trading yana da hadarin gaske sosai domin shi yanzu ne ake samu kudi masu yawan gaske sannan kuma yanzu ake rasa kudi gaba daya, sabida forex trading ba kamar coin din crypto currency bane wanda yake ƙarƙashin bitcoin. shi forex wajen nasara ne ko faduwa hakan ne yasa ake taka tsantsan wajen yin amfani da shi amma akwai inda zaka iya amfani da coin wanda yake ƙarƙashin bitcoin kayi irin. Forex Trading. Dashi wanda ake kira da Futures Trading. shima yana da hadarin gaske sosai domin shima yana kamanceceniya da Forex Trading

Yana da kyau ga duk wanda zai shiga Forex Trading da makamancin Forex Trading to fa yayi karatu sosai idan ba haka ba zai iya rasa kuɗaɗan sa gabaki daya


Domin Neman Ilimin Trade Cikin Yaran Hausa Za'a Iya Join Na Groups Namu

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇



 








Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad